Babban daraktan hukumar tace fina-finai da dab’u na jihar Kano Ismail Na’abba Afakallah, ya ce Rahma Sadau, na da ‘yancin fitowa a fina-finai ko daukar nauyi fina-finai karkashin jagorancin hukamar tace fina-finan kuma ba wata kungiya da zata hana ta fitar da fim.
Ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da Wakiliyar DandalinVOA inda ya bayyana cewa tun da farko da kungiyar MOPPAN ta dakatar da Rahma Sadau, hukumar tace fina-finan sai da ta binciki fina-finan jarumar tare da gindaya mata wasu sharudda da ta kiyaye na baiwa al’umma hakuri sa’annan ne hukumar ta bata damar gudanar da fina-finanta kamar kowa.
Shugaban ya kara da cewa aikin hukuma daban sa’annan ayyukan kungiyar ‘yan fim daban, inda ya kara da cewa tunda Rahma Sadau, ta kiyayye da dukkanin sharuddan da aka gindaya mata, a hannu guda, hanata gudanar da fina-finai zalunci ne.
Ya kuma bayyana ire-iren tsare-tsare da hukumar ta fito da su domin inganta harkar fina-finai a yunkurin tsaftace masana’antar, dan haka ne ma aka fito da sababbin hanyoyi ko tsare-tsaren fitar da fina-finai tare da magance matsalolin ‘yan downloading.
Afakallah a yayin da yake tsokaci dangane da ‘yan downloading, ya kara da cewa shigo da su harkar zata tsaftace harkar tare da basu dama wajen gudanar da sana’oinsu.
Your browser doesn’t support HTML5