Yau 5 ga watan Oktoba sauran daliban makarantar Chibok da har yanzu ke hannun 'Yan Boko Haram suka cika kwanaki 2000 a hannun mayakan.
Madam Maureen, daya daga cikin jiga-jigan Kungiyar BBOG masu fafutukar kwato sauran ‘yan mata 112 da su ka rage a hannun ‘yan Boko Haram, ta raira wakokin kungiyar ta kuma yi jawabi a wurin taron tunawa da ‘yan matan,da suka cika shekaru 5 da rabi a hannun ‘yan ta'addan.
Dr. Emman Usman Shehu, ya fadi cewa an sami nasara a yakin kwato ‘yan matan amma irin ta mai hakar rijiya, domin har yanzu gwamnatin Buhari ba ta cika alkawalin da ta yi wa 'yan kasa ba, a ganinsa wannan gazawa ce sosai a bangaren gwamnati. Ya kuma yi kira da cewa su ‘yan kungiyar za su ci gaba da gwagwarmayar neman ceto 'yayan talakawa da ake garkuwa da su domin gwamnati ba ta ma maganar su, amma a cewar Dr. Usman, ba za su manta da 'yan matan ba saboda ci gaba da rike su abin kunya ne ga kasa kamar Najeriya.
Shi ma Mr. Yakubu Kabu mahaifin Dorcas Yakubu, daya daga cikin ‘yan mata 112 da har yanzu suke a hannun ‘yan ta'addan, ya ce tun da ana labarin suna da rai, ya yi imani wata rana 'yar shi za ta dawo, amma yana mai rokon gwamnati da ta dauki mataki na gaggawa wajen taimakawa iyayen 'yan matan wadanda suka rage wajen yi masu bayanai masu kwantar da hankali, saboda a cewarsa, matar sa da yawancin wadanda ‘yayan su ke daji, a yanzu haka suna fama da ciwon zuciya da kuma ciwon hawan jini da ka iya kashe su a koda yaushe.
Your browser doesn’t support HTML5