Rade-Radin Bullar Mayu A Malawi Ya Janyo Kashe-Kashe

Rade-radin dake yawo game da bullar mayu, ko kuma wasu mutane dake sauya kama su zamo jemagu suna tsotse jinin mutane, ya janyo karuwar kashe-kashe a kasar Malawi.

Daga watan Satumba zuwa yanzu, an jefe mutane akalla 9 har lahira a kasar a saboda ana zarginsu da maita ko shan jinin mutane, yayin da ‘yan sanda suka kama mutane kimanin 140 ana tuhumarsu da aikata irin wannan kisa.

A ranar 19 ga watan nan na Oktoba ma, gungun mutane a Blantyre, babban birnin kasar ta Malawi, sun jefe wani matashi mai shekaru 22 da haihuwa, wanda kuma yake fama da cutar farfadiya, suka kashe shi bisa zargin cewa yana shan jinin mutane. Har ila yau a wannan rana, an kashe wani mutumin shi ma bisa zargin yana da irin wannan maitar.

Wata mata mai suna Aida Chikopa ta fadawa shugaba Peter Mutharika wanda ya ziyarci yankin domin ganewa idanunsa wannan lamarin cewa ita ma haka kawai ta ga jinni yana fitowa ta hancinta, kuma da ta tashi mijinta suka duba ba su ga komai ba. Da shugaban ya nemi Karin bayani, sai ta kasa bayyana mata.

‘Yan sanda da likitoci suka ce wannan labari na mayu masu tsotse jinin mutum, jita-jitar karya ce kawai. Sufeto janar na ‘yan sandan Malawi, wanda ke tare da shugaban, yace wannan matar tana fama da habo ne kawai, ba wai wasu mayu ne suka kama ta ba.