Rabiu Abdullahi Usman, mawaki ne na fadakarwa, siyasa da kuma soyyaya, mussaman hanyoyin isar da sakonin da zasu amfanar da matasa kamar yadda yake fade.
Ya ce yana fadakar da illolin shaye-shaye, wakokin zaman lafiya, a wannan lokaci na kakar zabe domin kwantar da hankali 'yan Nijeriya, su so juna tare da tabbatar da an samu zaman lafiya, da gudun tada zaune tsaye.
Rabiu Fagge, ya kuma ce ya kan yi wakokin zaman lafiya tsakanin matasa, sabo da yawaitar mace macen aure, sabanin da ake samu da zarar an yi aure.
Ya kan yi waka akan matsalar nan ta kwaya, wadda kafin yayi nisa da hada wakar ne ya ziyarci hukumar yaki da kwaya, domin samun cikakken ilimi kafin fitar da wakar, amma hakar sa bata cimma ruwa ba, domin bai samu goyon bayan da yake bukata ba.
Rabiu dai ya fara waka shekaru 15 da suka wuce, kuma kamar kowanne mawaki mai tasowa, ya fuskanci 'yar matsala da abokan aiki, ko mawaka sun dan nuna masa cewar yayi saurin shiga harkar ta waka, akan haka ne basu bashi gudunmuwar da ta da ce ba.
Mahaifiyarsa ta mara masa baya a lokacin da ya fara waka, haka zalika mahaifin sa ma yayi masa wa’azi na rike gaskiya da amana.
Your browser doesn’t support HTML5