Shugaban kungiyar kasashen Turai Donald Tusk da Firaministan Turkiyya Ahmed Davutoglu sun kira wannan yarjejeniya a matsayin wata babbar hobbasa. Davutoglu yace wannan abin tarihi ne ga kasarsa da Kungiyar Tarayyar Turai.
Wannan yarjejeniya zata shiga aiki gadan-gadan a gobe Lahadi, inda dukkannin ‘yan gudun hijirar Syria da wasu kasashe da suka shiga kasar Girka ba da izini ba, za a aika da su Turkiyya bayan an musu rijista tare da amincewa da neman mafakar da suka yi.
Sannan za a raba yawansu daidai wadaida ga kasashen Turai guda 28. Fiye dai da ‘yan gudun hijira Miliyan da Dubu Dari Biyu ne suka kutsa cikin Turai musamman ma ta kan iyakokin tekun kasashen Girka da Italiya.
Kama tun daga shekarar 2015, bayan mutuwar wasunsu kimanin guda dubu hudu da suka nutse a teku a kokarinsu na tserewa masifar yake-yaken da ake fama da ita kasashensu.