Ra’ayoyin ‘Yan Najeriya Dake Kudu Maso Gabas Kan Dage Zabe

Shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmood Yakubu

Dage zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin kasa da hukumar zabe ta kasa INEC ta yi, yanzu ya janyo fushi daga masu ruwa da tsaki da kuma sauran al'ummar kudu maso gabashin Najeriya.

Galibi mutane a Kudu maso Gabashin Najeriya sun fi nuna damuwa da zaben shugaban kasa da ya kamata a gudanar yau Asabar kamar yadda jadawalin zabe daga hukumar ya tanadar.

Lamarin nan dai ya sa har kungiyar Ohanaeze Ndigbo fitowa, inda sakataren yada labarai na kasa na kungiyar, Barista Uche Achi Okpaga ya kwatanta dage zaben a matsayin abin takaici.

Ya ce, "Abin takaici ne cewa bayan an sa 'yan Najeriya su fito su yi zabe sai kwatsam, 'yan sa'o'i kafin a yi zabe, aka ce musu an dage zaben. A wasu rumfunan zabe, jama'a sun riga sun fito daruruwansu don su yi zabe, sai kawai suka ji cewa an dage zabe. Wannan abin kunya ne ga kasarmu. irin wannan abin ne ya sa muke ta korafi cewa ba abin da ke tafiya a kasar. Babu yarda da hukumar zabe ta INEC, babu yarda da fadar shugaban kasa, kuma yanzu sun hakikanta hakan. Sun wanke 'yan Najeriya."

Shi kuma Ifeoma Nwafor cewa ya yi, "Kamar hukumar INEC da wasu 'yan siyasa na yunkurin murda zaben ne ya sa suka dage zaben da gangan. Kuma idan basu dage zaben ba, baza su iya cimma muradin kansu ba."

Justice Okorie, cewa ya yi "Dage zaben ya gurgunta komai saboda yawancin mu mun baro wurare daban-daban ne muka dawo gida da sa ran cewa zamu yi zabe yau, sai kawai da sassafen nan suka dage zabe. Ya kamata a sanar da dagewar da wuri don mu kasance a duk inda muke a sassar kasar, ba tare da kashe kudin mota ko sanya rayuwarmu cikin wani hatsari ba."

Ga rahoton wakilin mu Alphonsus Okoroigwe daga Owere:

Your browser doesn’t support HTML5

RA'AYIN 'YAN KUDU A KAN DAGE ZABE