Ra’ayoyin ‘Yan Arewa Kan Dokar Hana Shigowa Da Motoci Ta Kan Iyakokin ‘Kasa

Sanarwar da gwamnatin Najeriya ta bayar kan batun hana shigowa da motoci ta kan iyakokin kasar wadda zata fara daga ranar daya ga watan shekara mai zuwa abu ne da wasu ke yabawa dashi, a yayin da wasu kuma ke bayyana hukuncin da cewa matakine na hanasu sana’arsu.

Kamar yadda mazauna gabar tuku ke bayyana farin cikinsu ga wannan hukunci su kuwa ‘yan Arewacin kasar wadanda basu da hanyoyin ruwa ke bayyana takaicinsu game da hukuncin da gwanatin ta dauka.

Mataimakin kungiyar masu saye da sayar da motoci na kasa Alhaji Adamu Aliyu ATM, mai kula da shiyyar Arewa maso Gabas yace wannan shiyya bata da wata tashar jirgin ruwan da za a iya shigo da kayayyaki ba tare da wahala ba, inda ya roki gwamnatin tarayya domin samar da sauki ga harkokin kasuwancinsu.

A gefe daya kuma kungiyar masu harkar shigowa da motoci a jahar Bauchi ta gudanar da taron manema labarai kan wannan batu. Alhaji Kabiru Sa’idu shugaban masu sayar da motoci a jahar Bauchi, yace wannan lamari ya taba su matukar gaske, domin aikinsu shine zuwa Kwatano su sayo motoci su kuma bi duk ka’idar gwamnati wajen shigowa da motocin, amma yin hakan zai hana mutane da yawa neman abincinsu.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ra’ayoyin ‘Yan Arewa Kan Dokar Hana Shigowa Da Motoci Ta Kan Iyakokin ‘Kasa - 2'27"