Ra'ayoyin Jama'a Kan Dokar Ta Baci A Adamawa

  • Ibrahim Garba

Wasu sojoji a Yola, hedikwatar jihar Adamawa ke sintiri

Wasu mutane a Yola, hedikwatar jihar Adamawa, sun bayyana ra'ayoyinsu game da yadda dokar ta baci ke gudana a jihar da kuma yadda ta shafe su
Wasu mazauna Yola, hedikwatar jihar Adamawa, daya daga cikin jihohi uku da aka kafa dokar ta baci cikinsu, sun bayyana yadda jami'an tsaro ke aiwatar da dokar ta baci a jihar da kuma yadda dokar ke shafarsu.

Wakilinmu a Adamawa Ibrahim Abdul'aziz ya ruwaito wani malamin addinin Musulunci mazaunin birni Yola na cewa lokacin dokar ta bacin na hana Musulmi sukunin idar da Sallah kamar yadda ya wajaba a kansu. Shi ma wani mazaunin garin na Yola mai suna Yakubu Musa ya ce sun yi mamakin yadda aka sa jihar Adamawa cikin jihohin da ke bukatar dokar ta baci. To amman su na fatan wannan shi ya fi alheri garesu. Ya ce dokar na shafar 'yan kasuwa, musamman ma wadanda sana'arsu ta fi kyau da dare kamar masu shayi da suya da dai sauransu. Ya ce ya zuwa yanzu dai sojojin na aiwatar da dokar yadda ya kamata, kuma su na fatan za su cigaba da hakan.

Shi ma wani dattijo mai suna Ahmadu Alhaji ya gaya ma Ibrahim Abdul'aziz cewa so ba 'yan Boko Haram su ka dame su ba, barayi ne matsalarsu.

Your browser doesn’t support HTML5

Ra'ayoyi Kan Dokar Ta Baci A Jihar Adamawa - 2:34