'Yan Ghana mazauna Najeriya sun bi sawun takwarorinsu dake zaune a kasarsu inda suka bayyana ra'ayoyinsu dangane da mulkin sabon shugaban kasarsu Nana Akufo-Addo yayinda ya cika kawanaki dari da kama mulki.
Wani da ya fito daga Ghanan watanni biyu da suka gabata yace kowa yana murna shugaban ya hau mulki amma akwai sauran gyara da shugaban zai yi. A ganinsa shugaban yana cikin yin gyaran.
Akwai gyaran hanyoyi da yakamata a yi. Akwai gyaran harkokin ilimi saboda wai makarantu sun yi tsada, farashin abinci sai kara tashi ya keyi tare da karancin kudaden waje.
'Yan kasan suna bukatan ya taimakawa 'yan kasuwa kanana da manya domin farfado da tattalin arziki. Dangane da samar da ayyukan yi har yanzu 'yan kasar sun ce basu gani a kasa ba.
A cewarsu shugaban ya fara cika wasu alkawuran da yayi lokacin da yake fafutikar neman zabe.
Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5