Ra'ayoyin 'Yan Najeriya Kan Nadin Sabbin Ministoci

Lokacin da shugaba Buhari yake rantsar da ministocinsa a watan Nuwambar shekarar 2015 a wa'adinsa na farko.

Yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayinsu dangane da jerin sunayen da Shugaba Muhammadu Buhari ya mika wa majalisar dattawan kasar, domin ta amince ya nada su ministoci.

A baya dai Shugaba Muhammadu Buhari ya cewa wannan karan zai tabbatar da ya nada mutanen da ya sani a matsayin ministocinsa, yayin da yake cewa galibin ministocin da ya yi aiki dasu a wa’adin mulkinsa na farko bai sansu sosai ba, Jam’iya ce ta tsaida su.

A halin yanzu dai Shugaba Buhari ya tura sunayen mutane 43, wanda a ciki an samu tsofaffin Ministocinsa 10 wadanda suka yi aiki da shi a wa'adinsa na farko. ciki akwai tsohon ministan shari’a Abubakar Malami, da tsohon ministan yada labarai Lai Muhammed. Bakwai daga cikin adadin ministocin 43, mata ne.

Sai dai wasu daga cikin 'yan kasar sunyi korafin cewa akwai gyara saboda shakkunsu game da nagartar wadanda shugaban ke kokarin nadawa.

Saurari Rahoton Mahmud Ibrahim Kwari, Cikin Sauti

Your browser doesn’t support HTML5

Ra'ayoyin 'Yan Najeriya Kan Nadin Sabbin Ministoci