Ra'ayoyin Al'ummar Niger Game Da Badakalar Ma'akatar Tsaron Kasar

Biyo bayan sanarwar da gwamnatin Niger tayi, gameda batun zarge-zargen almundahana a ma’akatar tsaron kasar da kuma hukuncin da ya ayyana zai dauka kan duk wanda aka samu da hannu cikin wannan badakalar, al’ummomin Niger suna ta bayyana ra’ayoyinsu akan wannan batu.

Inda mafi akasarin al’ummar kasar suka nuna rashinamincewarsu da matakin da gwamnati ta ce zata dauka ba, kasancewar basu bada mahimman bayyanai game da wanda ake zargi ko laifin da aka aikata ba, kana, sun nuna cewa har in adalci gwamnati takeso tayi, sai ta hannunta wannan batu ga kotun kasar.

Wasu daga cikin al’umma sun dauka tamkar, gwamnati wasa da hankalin al’umma takeyi, domin ya zama tamkar kamar rarashin mutane da suka aikata laifin gwamnati keyi maimakon ake an gurfanar da su a kotu don dayi aikinta. Musammamn ma idan akayi la’akari da irin laifin da aka aikata na yiwa kasa zagon kasa wajen sayo makamai marasa inganci alhalin gwamnati ta samar da wadatattun kudade da za a sayo kayakin yaki.

A saurari cikakken rohoto Yousoufu Abdoulayi: