Ana ci gaba da samun ra’ayoyi masu karo da juna a ciki da wajen Amurka, kan yadda Amurkan ta amince cewa yankin Tuddan Golan ko kuma Golan Heights mallakar Isra’ila ne.
Yayin da wasu ke cewa, matakin da Amurka ta dauka zai iya rura wutar gabar da ke tsakanin Isra’ila da Larabawa, wasu kuwa cewa suke matakin ba zai sauya komai ba.
Amurka dai ita ce kasa ta farko da nuna goyon baya Isra’ila ta mallake yankin na Golan, yayin da sauran kasashen duniya ke kallon yankin a matsayin wanda ke karkashin kulawar Isra’ilan.
A gefe guda kuma, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi kira da akai zuciya nesa a yankin zirin Gaza, bayan da aka kwashe kwanaki Isra’ilan na kai hare-haren sama, a matsayin martani ga harin roka da aka harba cikin Isra’ila daga yankin Palasdinawa.
“Mun fito karara mun yi Allah wadai da harin rokan da aka kai, amma a yanzu, mun ga ya dace a kaucewa rura wutar wannan rikici.” Inji Guterres.