Ra’ayoyi Mabanbanta Kan Haramta Hakar Ma’adinai a Zamfara

  • Murtala Sanyinna

Mutane fiye da 200 suka rasa muhallansu a Karamar Hukumar Maru a Jihar Zamfara.

Tun bayan da gwamantin tarayya ta haramta ayyukan hakar ma’adinai a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, mazauna yankin da masana da sauran al’umar Najeriya ke ta bayyara ra’ayoyi masu kishi da juna.

Yayin da wasu key aba daukan wannan mataki, wasu kuwa cewa suke matakin haramta ayyukan ba zai sauya komai ba kan rikice-rikicen da jihar ke fama da su.

A farkon makon nan ne, Sifeto Janar na ‘yan sanda Najeriy, Muhammad Abubakar Adamu ya ayyana haramta aikace-aikace, a wani mataki na fara shawo kan hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa jihar da kuma matsalar garkuwa da mutane da ake yi a yankin.

Wasu da dama, sun dasa alamar tambaya kan daukan wannan mataki bisa alakar da ke tsakanin aikin hakar ma’adinan yayin da wasu ke ganin akwai kwakkwarar alaka.

“Abin da zai b aka mamaki shi ne, wannan tashin hankali ya karade lungu da sako a jihar Zamfara, amma har yanzu cikin ruwan sanyi ana harkar hako zinaren nan, kuma ba ka taba ji an ce an kai masu hari ba.” Inji Bashir Muhammad Achida, malami a fannin nazarin tsimi da tattalin arziki na jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto.

Sai dai masu fashin baki a fannin tsaro na ganin, wannan mataki ba zai yi wani tasiri, kuma ba shi da alaka da tashin hankalin.

“A nawa ganin, babu wani tasiri da wannan mataki zai yi, mutanen nan da ke gudanar da wadannan abubuwa (hare-hare) Fulani ne makiyaya tun bayan da aka fara sace masu dabbobi, har suka kai ga wannan lokaci da aka fara kama mutane ana neman kudin fansa.” A cewar wani babban jami’in sojin Najeriya, Aminu Bala Sokoto mai ritaya.

Saurari cikakken rahoton Murtala Faruk Sanyinna:

Your browser doesn’t support HTML5

Ra’ayoyi Mabanbanta Kan Haramta Hakar Ma’adinai a Zamfara - 3'03"