Yayin da shirye shiryen Gasar Cin Kofin Duniya ta 22, wadda za a yi a kasar Qatar, daga ranar 20 ga watan nan na Nuwamba zuwa 18 ga watan Disamba, ke dada kankama, manyan kafafan yada labarai na kasa da kasa, ciki har da Muryar Amurka, su ma sun je don sanar da duniya abubuwan da ke gudana. Hasali ma, jiya ne mai wakiltar Sashin Harsunan Afurka na Muryar Afurka, Khali Abdu, ya isa Qatar don ba ku bayanan abubuwan da ke gudana.
Dazun nan Babbar Editar Sashin Hausa, Alheri Grace Abdu, ta tambaye shi inda aka kwana a shirye shiryen gasar; sai ya ce: har yanzu ‘yan kallo, da ‘yan jarida, da nau’ukan ma’aikata masu nasaba da wannan gasar daga kasashe daban daban, da sauran masu ruwa da tsaki na cigaba da dunguma zuwa Qatar wurin wannan gasar da za a fara ranar Lahadi kuma tuni gari ya yi cinkus.
Khali ya ce za a fara fafatawa ne tsakanin Qatar da Ecuador ranar Lahadi, kuma har ‘yan Ecuador din sun fara isowa yayin da ‘yan Qatar kuma ke cigaba da shiri.
Ya ce hatta ‘yan kasashen da ba su cikin gasar, kamar Najeriya, Pakistan, Bangladesh da dai sauransu na ta isowa saboda, ko ba komai, an kai gasar ne a kasar da ba kasafai akan kai irin wannan wasan ba. Don haka za su ga wasu abubuwan da ba su saba gani ba.
Wakilin na Sashen Harsunan Afurka na Muryar Amurka a gasar ya tabbatar cewa lallai kasar ta Qatar ta dau matakin rage yawan mutanen da ke shigowa kasar saboda kar a ma ta yawa. Ta na mai bayar da fifiko ga masu zuwa don wannan gasar.
Ya ce sai daga ranar 2 ga watan Disamba za a sassauta matakan takaita yawan masu shigowa kasar, saboda ana kyautata zaton cewa zuwa lokacin wasu da dama, musamman ma wadanda su ka fito daga kasashen da ba su cikin gasar, sun bar kasar.
Saurari kashi na farko na wannan hirar:
Your browser doesn’t support HTML5