Pyongyang Ta Gano Baraguzen Jirgi Marasa Matuki A Babban Birnin Kasar

Smoke rises from factories over central Pyongyang, North Korea, Dec. 9, 2011. (AP)

Koriya Ta Arewa tayi ikirarin gano wasu tarkacen akalla jirgi mara matuki guda na sojojin Koriya Ta Kudu a babban birnin kasar Pyongyang, tare da kafa wasu hotunan jirgin da masu sharhi suka tabbatar cewa lallai na KTK ne.

KTA tayi ikirarin gano wasu tarkacen akalla jirgi mara matuki guda na sojojin KTK a babban birnin kasar Pyongyang, tare da kafa wasu hotunan jirgin da masu sharhi suka tabbatar cewa lallai na KTK ne.

Kasar ta Arewa data mallaki makaman nukiliya a ‘yan kwanakin nan, ta zargi Seoul da yin amfani da jirage marasa matuka tana jibge takardun farfaganda a babban birnin kasar.

Mai Magana da yawun ma’aikatar tsaron Pyongyang ya ce hukumomin tsaro sun gano wasu tarkacen wani jirgi mara matuki da ya fadi a yayin da suke kewaye babban birnin kasar ta KTA a ranar 13 ga watan Oktoba, abinda kafar yada labaran kasar KCNA ta ruwaito Kenan.

Binciken da KTA ta gudanar kimiyance ya tabbatar da cewa lallai tarkacen jirgi marasa matukin na ROK ne, a cewar wani mai Magana da yawun kasar da ba a bayyana sunan sa ba, sai dai yayi amfani da inikiyan jami’an KTK.#