Shugaba Trump yayi ta kare kansa a wannan satin bayan da kafafen yada labarai suka bada rahoton cewa ya bada bayanan sirri na tsaro ga Lavrov da kuma Jakadan Rasha Sergei Kislyak.
WASHINGTON D C —
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yace shugaba Trump bai bada bayanan sirri ga Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ba a yayin ganawar su ta satin da ya gabata a Washington, haka kuma yana da cikakken rubutun tattaunawar da zai iya nunawa a matsayin shaida.
Putin ya fadi hakane a yau Laraba yayinda yake tare da Firai Ministan Italy Paolo Gentiloni, Putin yace Lavrov bai fada masa sirrin da ake ta yayatawa ba. Kuma zaiyi farin cikin bada bayanin tattaunawar a rubuce.
Shugaban kasa da mataimakan sa sun musanta Trump ya bada bayanin da zai iya saka hanyar da ake samun bayanan tsaron cikin hadari. Mai bada shawara akan Harkokin tsaro H.R. McMaster ya kira tattaunawar Trump da Jakadaun Diflomasiyyar Rasha “Cikakkiya wadda ta dace”