Prime Ministan Kasar Lebanon Saad Hariri Yana kasar Faransa

  • Ladan Ayawa

Shugaban Fransa Emmanuel Macron

Yanzu haka Prime Minister kasar Lebanon Saad Hariri na Faransa, inda suke ganawa da shugaban kasar Emanuel Macron,sai dai gwamnatin kasar ta Lebanon tace tana bukatar Hariri da ya dawogida.

Prime Ministan Lebanon Saad Hariri yanzu haka yana Elysee fadar gwamnatin kasar Faransa inda suke tattaunawa da shugaban Kasar na Faransa Emanuel Macron, wanda ya yi masa tayin taimaka masa domin shawo kan matsalar dambaruwar siyasar da kasar tasa afka.

Idan dai ba a manta ba a cikin farkon wannan watan ne Hariri ya bayyana murabus din sa a gidan wani talabijin dake kasar Saudi Arabiya abinda ya haifar da rudu da damuwa a cikin kasar ta Lebanon.

To sai dai kuma a yau asabar din nan kanfanin dillacin labarai na kasar ta Ambato Hariri na cewa, Ya kira shugaban kasar ta Lebanon Michel Aoun ya shaida masa cewa yana dawo wa cikin kasar a sati mai zuwa domin ya halarci bikin samun ‘yancin kasar.

Sai dai abinda ba a sani ba shine ko Hariri ko kuma mai masaukiin nasa,wato Macron zasu ce wani abu game da wannan rahoton da kanfanin dillacin labaran ya wallafa.

Sai dai Macron ya fada a Sweden cewa anyi wa Hariri marhabin ne a Faransa a matsayin Prime Ministan Lebanon tunda ko shugaban kasar bai amince da murabus dinsa ba a hukumance.