Kungiyar kwallon kafa ta Plateau United ta Lashe gasar firimiya lkig na Najeriya, na bana wanda aka kammala a tarayyan Najeriya, watau (Nigerian Professional Football League).
Inda kungiyoyin kwallon kafa ashirin da suka fito daga sassan kasar suka fafata, Kungiyar kwallon kafa ta Plateau United, dake garin Jos, a arewacin Najeriya ita ta lashe gasar na bana a karon farko tunda aka kafa kungiyar fiye da shekaru arba’in. a lokacin ana kiranta JIB, Strikers Fc. Kafin da ga bisani ta Koma Plateau United, a shekara ta 1991.
Kungiyar MFM FC, dake garin Lagas ita ta biyo bayan a mataki na biyu da maki 62, sai Enyimba da ta kare a matsayi na uku da maki 61.
Akwa United, nada maki 60, sai Nasarawa United 56, El-Kanemi 56, Lobi Stars, 54, kano Pillars 54, Kungiyar Ifeanyi Ubah ta kare a mataki na tara da maki 54, Sunshine da maki 54, ita ma Niger Tornadoes da maki 54. a mataki na sha daya.
Abia Warriors ta kasance a mataki na sha biyu da maki 53, Enugu Rangers da maki 53 ,Wikki Tourist na garin Bauchi, tana mataki na sha hudu da maki 53.
Your browser doesn’t support HTML5
Sauran kungiyoyin sun hada da Rivers United da ta kare a mataki na sha biyar da maki 52, sai Kastina United da maki 52 a mataki na sha shida.
Kungiyoyi hudu sun Koma wasan kasa da firimiya lig. sakamakon rashin tabuka abun kirki a wasan na bana.
Kungiyoyin sune Shooting Stars, na garin Ibadan a mataki na sha bakwai da maki 50, ABS Fc, na garin Ilorin da maki 49, Gombe United, daga jihar Gombe, tana da maki 43 sai kungiyar kwallon kafa ta Remo Stars na garin Shagamu, da ta karkare a mataki na ashirin da maki 29.
An fafata wasanni 380, a cikin sati talatin da takwas da akayi ana gwabzawa a tsakani.