Firai Ministan Spain ya gargadi majalisar dattawan kasar a yau Juma’a da ta dauki wani matakin doka na musamman da zai ba gwamnatin tsakiya hurumin kwace ikon ncin gashin kai na Catalonia, a wani yunkurin takawa yankin mai neman ballewa daga kasar burki.
WASHINGTON DC —
Mariano Rajoy ya fadawa sanatocin cewa kasar Spain na huskantar babban kalubale da ba a gani a cikin wannan lokaci ba, ya kara da cewar abin da ke faruwa a Catalonia babban take dokoki da bijirewa demokaradiya da take hakkin kowa da zai yi mummunar tasiri ne.
Rajoy yace idan majalisar ta amince da wannan bukata, matakin gwamnati na farko shine kwace yankin Catalonia da kuma korar shugaban Catalonia da ministocinsa.
Akwai maganar da ake yayatawa, cewa Catalonia tana shirin ayyana yancin kai a wani buki na musamman da yammacin yau Juma’a.
Dubban masu zanga zanga sun taru a kusa da majalisar dokokin Catalonia rike da tutocin yankin suna kira ga samun yanci da walwala da zummar ganin an ayyana kasa mai cikakken 'yanci.