PHCN: Ma'aikata Sun Shiga Yajin Aiki

congress letter to DOS

A lokacin shugaba Goodluck Jonathan gwamnatinsa ta ba 'yan kasuwa tsarin samar da hasken wutar lartanki

Amma kusan shekaru biyu da aka soma sabon tsarin yawancin 'yan Najeriya basu gani a kasa ba. Lamarin bai sake zani ba.

Rarraba wutar ga 'yan Najeriya har yanzu jidali ne. Kamfanonin da aka baiwa hakin rarraba wutar babu abun da su keyi illa tatsar makudan kudi daga jama'a ba tare da bada hasken wata ba.

Bisa ga ra'ayin wasu 'yan Najeriya wasu kamfanonin lantarkin sun nuna gazawarsu na iya biyan hakin ma'aikatansu. Tuni wasu ma'aikatan kamfanonin a jihohin kudu maso kudu suka shiga yajin aiki suna neman a biyasu hakinsu.

Ma'aikatan sun bukaci a biyasu albashinsu kana a maido da ma'aikatan da aka kora ba bisa kan ka'ida ba.

Wani a jihar Rivers cewa yayi yakamata ma'aikatan su shiga yajin aiki idan ba'a biyasu ba kuma an kori wasusnsu ba kan ka'ida ba.Yace ma'aikatan su ma suna da iyali da suke ciyarwa da kuma biyan wasu bukatu.

Jihar Rivers dai tana cikin wani hali na kwanaki da dama babu wutar lantarki.

To saidai wasu 'yan arewa mazauna jihohin Rivers da Bayelsa sun zargi ma'aikatan da neman shafawa gwamnatin Buhari kashin kaza. Kamata yayi tun lokacin da aka mikawa 'yan kasuwa kamfanonin lokacin shugaba Jonathan ya kamata su shiga yajin aikin saboda rashin biyansu.

Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto.

Your browser doesn’t support HTML5

PHCN: Ma'aikata Sun Shiga Yajin Aiki