Pepe na Portugal Ya Ce Alkalin Wasa Facundo Tella Ya Janyo Masu Shan Kashi a Hannun Morocco

  • Murtala Sanyinna

Ronaldo ya sha kuka yau

Yayin da Pepe ke zargin Alkalin wasa da taka rawa wajen rashin nasara da Portugal ta yi, shi kuma Cristiano Ronald, zubar da hawaye ya yi ta yi sharbe sharbe.

Morocco ta kafa sabon tarihi, na kasancewa kasa ta farko ta nahiyar Afirka da ta sami kai wa a matakin wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin duniya ta hukumar FIFA, bayan da a yau ta yi nasarar doke Portugal da ci 1-0 a wasan QF na gasar ta bana a Qatar.

Morocco din dai ta sami zura kwallon ne tun a cikin rabin lokacin wasan na farko, inda kuma ta rike tare da jure dimbin matsin lamba daga Portugal da ke kokarin farkewa, har ya zuwa karshen wasan.

Dan jarida kuma mai sharhi kan lamurran wasanni, Umar Faruk Bukkuyum, ya ce da ma ai a rina.

Wannan dai muhimmiyar nasara ce ga daukacin nahiyar Afirka, to amma kuma rana ce ta bakin ciki da bacin rai ga kasar Portugal.

Ba ma kamar shahararren dan wasan kasar Cristiano Ronaldo, wanda da alama wannan ce dama ta karshe da yayi fatan samun daga kofin na duniya, amma kuma hakan bai samu ba.

Ronaldo ya shigo wasan ne a zaman canji tun farkon rabin lokacin wasan na 2, amma kuma bai kai ga tasirin sauya sakamakon wasan ba.

Hakan ya sa shi zubar da hawaye cikin kuka da jimami a karshen wasan, a yayin da yake tafiya domin ficewa daga filin.

Morocco din dai za ta fafata ne a wasan kusa da ta karshe da duk wanda yayi nasara tsakanin Ingila da Faransa da yanzu haka suke can suna fafatawa.

A daya bangaren kuma dan wasan baya na kasar Portugal wato Pepe, ya dora alhakin kashin da kasar ta sha a hannun Morocco, akan alkalin wasan, Facundo Tello.

A wata zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala wasan, Pepe ya ta’allaka rashin nasarar da suka samu da halayyar alkalin wasan dan kasar Argentina, na yawan dakatar da wasan da yayi.

Ya ce yadda alkalin wasan yayi ta dakatar da wasan a lokuta da dama, ya haddasa kasar ta Portugal ta kasa sukunin wanzar da tsari da kuzarin ta.

Gasar ta cin kofin duniya ta bana dai na ci gaba ne da bayyana irin na ta mamakin da ta zo da shi, a inda ko a jiya Juma’a, kasar Brazil ta yi waje road a matakin na QF, bayan da ta sha kashi a hannun Croatia ta hanyar bugun penarity, bayan da wasan su ya tashi a kunnen doki da ci 2-2.

Saurari cikakken rahoton Murtala Faruk Sanyinna:

Your browser doesn’t support HTML5

12-10-2022 SPORTS.mp3