PDP Zata Duba Irin Gyaran da Zata Yi-inji Gwamna Babangida Aliyu

PDP

Kafin PDP ta fada cikin matsalar da ta shiga yanzu sai da wasu gwamnoninta bakwai suka fito fili suka bukaci a yi gyara amma aka ki kulawa da korafinsu.

Jam'iyyar bata tashi yin gyara ba sai da abubuwa suka tabarbare inda wasu gwamnonin suka balle suka shiga APC.Yanzu kamar ta kaiga durkushewa.

Gwamna Babangida Aliyu yace abubuwan da gwamnaonin suka fara ya kaiga juyin juya hali inda jam'iyyar ta yi asarar gwamnatin tarayya. To saidai inji gwamna Aliyu abunda ya faru Allah ne ya kaddaro.

Da ya juya kan cigaban dimokradiya gwamna Aliyu yace idan ana son a tabbatar dimokradiya ta kafu shi ne a yi zabe a kada gwamnati mai ci ta kuma mika mulki ba tare da wani ja-in-ja ba.

Yanzu abun da PDP zata yi shi ne sai 'yan jam'iyyar su koma gida su sake lale. Su duba su gani wane irin gyara zasu yi da nufin farfado da jam'iyyar yadda zata iya tsayawa zabe a shekarar 2019 ta kuma yi nasara. Gwamna Aliyu yace suna da shekaru hudu su shirya.

A kan kiran da aka yi cewa shugaban PDP Alhaji Adamu Mu'azu ya sauka daga kujerarsa sai gwaman Aliyu yace a Ingila duk shugabannin jam'iyyun da suka fadi zabe sun dauki alhakin faduwarsu sun kuma yi murabus tunda a lokacinsu ne abun ya faru.Sabili da haka tunda a lokacinsa PDP ta fadi zabe to sai ya bada wuri wani ya shugabanci jam'iyyar zuwa ga nasara. Yace haka ake yi koina.

Dangane daga inda zasu fara gyaran sai gwamnan yace zasu fara daga kananan mazabu zuwa kananan hukumomi har su kai tarayya. Inji shi rabin wadanda suka koma APC zasu dawo.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

PDP Zata Duba Irin Gyaran da Zata Yi-inji Gwamna Bababngida Aliyu