Jam'iyyar adawa ta DSP tayi gangami domin karbar sabbin shigar a Jalingo.
WASHINGTON, DC —
Yayin da babban zabe ke kara matsowa, jam’iyar PDP mai mulki a Najeriya ta rasa rinjaye da ada take dashi a majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya, ana kasa da wata daya kamin a yi zabe.
Yanzu jam'iyyar APC ce take da rinjaye, tana da wakilai fiye da dari da 170, ita kuma PDP take da wakilai 160 da 'yan kai
A jihar Taraba jam'iyyar ta PDP ta rasawasu yayanta a jihar, ciki har da yan majalisar dattawa dana wakilai da kuma na majalisar dokoki, ko da yake jam’iyar PDPn tace bata razana ba.
Wannan ma na zuwa ne,yayin da ake takaddama da mukaddashin gwamnan jihar Sani Abubakar Danladi game takarar kujerar senata na mazabar Taraba ta arewa.
Your browser doesn’t support HTML5