Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya wato PDP ta sauya salon sukar hukumar zabe tunda aka sauya shugaban hukumar.
Ta bakin kakakinta na kasa Olisah Metuh can baya ta sha sukar shugabar hukumar ta rikon kwarya Amina Zakari da nuna cewa ba zata yiwa jam'iyyar adalci ba.
Olisah Metuh yace basu da wani dalilin kokwanto ko kushewa hukumar a karkashin sabon shugabanta Farsa Mahmud Yakubu. Amma bayan zabukan Kogi da Bayelsa jam'iyyar zata zauna ta yi nazari akan yadda ya jagoranci kowane zaben. Daga nan wai zasu bayyana matsayinsu.
Amma Olisah Metuh yace sabon shugaban INEC ya yi alkawarin yin adalci saboda haka zasu jira su gani.
Tsohuwar shugabar hukumar Amina Zakari ta bayyana wasu sabbin matakai da hukumar ta dauka saboda inganta zabe. Tace a Kogi da Bayelsa sun fitar da sanarwa cewa kowa na iya canza matsabarsa. Idan ma mutum ya canza gida yana iya yin zabe a sabon wurin da yake.Akan sanarda sakamakon zabe za'a iya yi da kwamfuta tun daga kananan hukumomi.
Hukumar zata gyra duk inda suka yi kurakurai. Zasu dinga shigar da sakamakon zabe tun daga kauyuka cikin kwamfuta yadda su kuma a hedkwatar hukumar zasu dinga gani. Idan an canza sakamako za'a sani nan take. Zasu kuma iya kamo duk wanda ya aikata laifin.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5