Bayan hukunci da kotun daukaka kara ta zartar na baiwa tsohon gwamnan jihar Borno Sanata Ali Madu Shariff nasarar kasancewa halartattacen shugaban jam’iyyar PDP na kasar, sai ga wata sabuwa ta kunno kai a jihar Borno, tsakanin ‘ya’yan jim’iyyar ta PDP.
WASHINGTON, DC —
Yanzu dai kan ‘ya’yan jam’iyyar ya rabu inda ko a jiya bagarorin biyu sun kira taron manema labarai a warare daban daban.
Bagaren Ali Madu Shariff, karkashin shugabancin Alhaji Shettima Shehu, sun gudanar da taronsu a wani dakin taro mallakar matar Ali Madu Shariff, tare da samun kariyar jami’an ‘yan Sanda da dama.
Daya bangaren kuwa masu goyon bayan Sanata Ahmed Makarfi, sun shirya gudanar da nasu taron a wani wurin taro daban kamar yadda yake dauke cikin takardan gayyata da suka aikewa manema labarai sai dai basu sami damar yi taron ba sakamakon haramtamasu taron da hukumar ‘yan Sanda tayi.
Amma duk da wannan haramci kungiyar ta gudanar da taron a wani wuri na daban.
Your browser doesn’t support HTML5