Wasu daga cikin 'yantakara ne dai suka bukaci masu zaben yantakatar na PDP da su yi amfani da katin zabe ko national ID card ko kuma E-pasport domin kada kuri’ar su.
Tsohon Ministan wajen Nigeria, Alh. Abubakar Tanko yace basu taba gani irin wannan tsari ba.
Lawyan PDP a jihohin Arewa ta tsakiyar Nigeria Barista Isyaku Barau yace tsarin bai sabawa kundun tsarin Mulkin PDP ba.
Ku Duba Wannan Ma Banky W. Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Karkashin Jam'iyyar PDP A LegasShugaban PDP na jihar Neja, Barista Tanko Beja yace za a gudanar da zaben a ranar Alhamis din nan.
Mataimakin Gwamnan Bayalsa Laurance Obarawharienwo da PDP ta turo jihar Nejan, ya tabbatarwa manema labarai cewa, zasu warware duk wasu matsalolin da su ka yi tarnaki a zaben.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5