Rikicin Shugabancin babbar jam’iyyar adawa ta PDP ya dau sabon salo, bayan da tsohon Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara Kan Siyasa Ahmed Gulak ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban jam’iyyar, ganin kotu ta zartas cewa yankin arewa maso gabas ne ya kamata ya fitar da ciyaman din jam’iyyar.
Wannan matakin da Gulak ya dauka ya kai ga rabuwar jam’iyyar gida biyu, wato da bangaren Ciyaman din da Gulak ya ce ya maye gurbinsa wato Uche Secondus da kuma bangaren shi Gulak din. Dama Gulak ya kai kara ne kan cewa kamata ya yid an arewa maso gabashi ya gaji Ahmed Mu’azuz amma bad an yankin da Secondus ya fito ba.
To saidai Mataimakin Sakataren Labaran PDP Abdullahi Jalo ya ce ba Gulak ne kadai ya dace ya gaji Ahmed Mu’azu ba; Shi kansa Jalon na daya daga cikin wadanda su ka cancanci yin takara. Don haka ya rage gwamnoni da sauran manyan ‘yan jam’iyya su zauna su yanke shawara.
Ga wakilinmu Nasiru Adamu Elhikaya da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5