Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP ta ce ta karce kasa a siyasance kuma zabe mai zuwa za ta ba da mamaki. Jam’iyyar ta yi wannan ikirarin ne a yayin babban taronta wanda ya haifar da sabon shugabanci.
Da ya ke mika shugabancin jam’iyyar a hukumance ga sabon shugaban jam’iyyar na kasa Prince Uche Secondus, tsohon shugaban na riko Sanata Ahmed Muhammed Makarfi ya ce ya karbi shugabancin nakasasshiyar jam’iyya, to amma ya mika kakkarfar jam’iyya ga sabon shugabanta.
Kan ko shin an yi taron na PDP da kuma yin sabbin shugabanni bisa ka’ida, wani lauya mai zaman kansa da ke Abuja mai suna Barrister Abubakar Kurawa ya ce a shari’ance ana iya cewa PDP ta yi daidai, to amma a siyasance da alamar ayar tambaya. To amma sai ya kara da cewa abu mafi muhimmanci shi ne jam’iyyar ba ta saba ma doka ba.
Your browser doesn’t support HTML5