PDP Ta Ce Daga Arewa Za Ta Fidda Da Dan Takarar Shugaban Kasa a 2019

Tutocin jam'iyyar PDP

Babbar jam'iyar adawa ta PDP a Najeriya, ta ce, daga yankin arewa za ta fitar da dan takarar da zai tsaya mata takara a zaben shugaban kasa a 2019.

A karon farko tun bayan da kotun kolin Najeriya ta yanke hukunci a rigimar cikin gida da ta ki-ci-ta -ki cinye wa a jam’iyyar PDP, jam’iyyar ta gudanar da taron majalisar zartaswarta ta farko a Abuja.

A taron ne jam’iyyar ta sake jaddada kudurinta na fidda dan takarar shugabancin kasar ga arewacin Najeriya.

Haka nan kuma taron ya kafa kwamitin sasantawa tsakanin ‘yayan jam’iyyar, musamman bangaren Senata Ali Modu Sheriff, da kuma bangaren Senata Ahmed Mohammed Makarfi, banagaren da kotun kolin Najeriya ya baiwaa nasara a hukuncin da kotun ta yanke.

Sakataren tsare-tsare na jam’iyyar PDP Abdul Ningi, ya gayawa Nasiru Adamu El-Hikaya cewa jam’iyyar a shirye take, ko kuma a ce tana jin nishadi gameda shirin karawa da ko wace jam’iyya a babban zaben kasa mai zuwa cikin shekaru biyu masu zuwa.

A tasa gudumawar, shugaban jam’iyyar PDP a jahar Zamfara Senata Mohammed yace duk da cewa shugabansu, tsohon Gwamnan jahar Mahmud Shinkafi ya canza sheka, a shirye suke wajen ci gaba da raya jam’iyyar a jahar.

Your browser doesn’t support HTML5

PDP Ta Ce Daga Arewa Za Ta Fidda Da Dan Takarar Shugaban Kasa a 2019