PDP Na Shirin Kwace Jihohin Jigawa Da Neja

Taron PDP na arewacin Najeriya

Yayin da jam'iyyu da 'yan sisaya a Najeriya ke ci gaba da yakin neman zabe domin tunkarar babban zaben kasar da za'ayi a watan gobe, Jam'iyyar hamayya ta PDP a jihohin Jigawa da Neja tace ta daura damarar dawo da gwamnati a wadanndan jihohi.

Gabanin zaben shekara ta 2015, Jam'iyyar ta PDP ce ke rike da kujerun gwamna da mafi yawan 'yan majalisar dokoki a jihohin biyu, sai dai a yanzu Jam'iyyar APC ce ke da gwamnati a jihohin.

Malam Aminu Ibrahim Ringim shine dan takarar gwamnan Jigawa a karkashin Inuwar Jam'iyyar PDP, yace mutanen Jigawa sun san abin da yake tafe da shi, yana mai cewa ya zo ne domin ya karasa ayyuaka da suka fara a baya kuma ya hada kan al’ummar jihar domin ya maido musu da martabarsu.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Jam'iyyar ta PDP a jihar Neja ke daukar matakan cin zabe a bana bayan ta sha kaye a shekarar ta 2015. Dr Mu'azu Babangida Aliyu shine dake zaman tsohon gwamnan jihar yace ya godewa Allah da aka samu wannan anji saboda mutan zasu ga kokarin da suka yi a baya.

Dr. Aliyu ya kar da cewa abubuwa dake faruwa a cikin wannan laokai yasa mutane sun gane cewa PDP tayi musu ayyuka sosai a baya. Ba batun gina hanyoyi kadai aiki ba, yanda zaka rike jama’a da girmamasu da kuma yi musu abubuwa da yakamata. Ya kuma ce gangaminsu ba zai kare a wurin taro kadai, zasu kuma shiga gida gida suna yada manufofinsu.

Galibi lokuta 'yan siyasa da sauran wadanda suka bada gudunmawa wajen yaki neman zabe a Najeriya suna korafin yadda sukan tura mota kuma ta bar su da kura bayan kafa gwamnati, lamarin da Malam Aminu Ibrahim Ringim dake yiwa Jam'iyyar PDP takarar gwamnan a Jigawa yace zai sauya.

Daga jihar Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko mana da wannan rahoto:

Your browser doesn’t support HTML5

PDP TA LASHI TAKOBIN KWACE JIGAWA DA NEJA