Tsohon dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, da kasar Ingila Paul Scholes, wanda kuma shine kocin kungiyar Oldham, ya ajiye aikinsa na horas da kungiyar tasa, bayan kwanaki 31 da kama aiki a kulob din.
Kocin Paul Scholes, mai shekaru 44 da haihuwa ya kama aiki a matsayin mai horas da kungiyar Oldham, a ranar 11 ga watan Fabrairun 2019, ya jagoranci wasanni bakwai da yayi nasara a wasa daya.
Scholes ya ce a cikin wata sanarwa da ya fitar ya yanke shawarar ya yi murabus daga matsayinsa ne tattare da "babban bakin ciki."
Kungiyar dai tana matsayi na 14 a teburin league Two na kasar Ingila. Ya fara wasansa tare da kungiyar Yeovil Town, da ci 4-1 wasanni uku da ya buga yayi canjaras, an samu nasara akansa a wasanni biyu ciki harda wasansa na karshe da Lincoln City ta doke su 2-0 a ranar Talata da ta gabata.
Paul Scholes yace "Ina fatan alheri ga magoya baya, 'yan wasa da ma'aikata- na kungiyar, kuma ina mai girmamawa garesu, da ci gaba da kallo da kuma goyan bayan kulob din."