Pastor T.B Joshua Yace Zagon Kasa ne da Aiyuka Irin na Ta’addanci

Wani bene mai hawa hudu da ake ginawa a unguwar Sabo Yaba, a birnin Lagos, ya rikito, a wani abu da ake dangantawa da rashin ingancin aiki.

Shugaban hukumar kiyaye muhalli da tsare tsare na jihar Lagos Michael Akinjide, yace “da rana nan ne dai muka samu labara na rugujewar wannan bene mai hawa hudu kuma muna gudanar da aiki na bada agajin gaggawa tare da nemu wadanda ke ciki idan har akwai domin rahotanin da muke samu na nuni da cewa babu kowa a cikin gidan a lokacin da ya rikito.”

Rugujewar wannan gini dai ba shine na farko ba a birnin Lagos, kuma yazo ne kasa da sao’I ashirin da hudu da hukuncin da wata kotu ta zartar na hukumta wani sanannen mai wa’azin Kirista mai suna T B Joshua, wanda ake zargi da mutuwar mutane dari da goma sha biyar (115), akasarinsu ‘yan Afirka ta Kudu, a Cocinsa a watan Satumban bara abun da ake dagantawa da rashin ingancin aiki.

Koda yake shukaban Cocin T.B Joshua, yace zagon kasa ne da aiyuka irin na ta’addanci.