Shugaban kasar Paraguay Horacio Cartes, a jawabin bude ofishin, ya bayyana cewa dauke ofishin jakadancin daga TelAviv zuwa Birnin Kudus na da dumbin tarihi kuma zai karfafa dangantaka tsakanin Isra’ila da kasar ta Paraguay.Frayim-ministan Isra’ila Benjamin Nethanyahu yayi maraba da wannan shawarar.
A satin da ya gabata ne Amurka ta kasance kasa ta farko da ta bude ofishin jakadanci a birnin Kudus inda ta cika alkawarin da shugaban kasar Donald Trump yayi a lokacin yakin neman zaben shi. Guatamela ta biyo sahun Amurka bayan kwanaki biyu.
Falasdinawa sun fusanata ainun da hakan, domin suna ganin gabashin Birnin na Kudus a matsayin babban birnin kasar ta Falasdinu a nan gaba, a yayin da su kuma Isra’ilawa ke ganin Birnin Kudus a matsayin babban birnin su mara rabuwa.