Paparoma Benedict Yayi fitar karshe a matsayin shugaban Katolika

Paparoma Benedict yana jawabin sallama

Paparoma Benedict ya yi fitarsa da gudanar da aiki na karshe a bainin jama’a a matsayin shugaban darikar Katolika kafin ya sauka daga mukamin gobe alhamis.

Paparoma Benedict ya bayyana a dandalin St. Peters dake birnin Roma yau Laraba inda ya jagoranci addu’oi ya kuma gana da membobin darikar karo na karshe. An raba kimanin tikiti dubu hamsin yayinda jami’ai suke kyautata zaton sama da adadin zasu halarci addu’oin.

Da yake jawabi ga taron jama’ar, paparoma Benedict yace duk da kalubalai da ikilisiyar ta fuskanta karkashin shugabancinsa, Allah ba zai bari darikar ta durkushe ba. Yace ya san irin nauyin shawarar da ya yanke ta yin murabus, sai dai ya shaidawa membobin darikar cewa, ya yanke wannan hukumcin ne da nauyin zuciya da kuma kamilci a ruhunsa. Yace yana da kyakkyawan karfin guiwa a kan kamomar ikilisiyar Katolika.

Tun farko Paparoman ya zaga kewayen dandalin St. Peters a cikin wata motar gilashi ya rika gaida dandazon jama’ar da suka taru da hannu, loto-loto kuma ya rika tsayawa yana yiwa jarirai da ake mika masa daga cikin jama’a addu’a.

Paparoma yakan fita ya yiwa jama’a jawabi mako mako, sai dai wannan jawabin na karshe ya dauki hankalin jama’a fiye da yadda aka saba.