Paparoma Benedict ya kalubalacin Lebanon ta zama abin koyi a fannin zaman lafiya

Paparoma Benedict

Paparoma Benedict ya yi kira ga kasar Lebanon ta zama abin koyi a fannin zaman lafiya da bada ‘yancin addinini a gabas ta tsakiya da ake fama da tashin hankali.

Shugaban darikar katolikan ya gana da shugabannin kasar Lebanon da na addinai yau asabar a fadar shugaban kasa dake birnin Beirut inda mutane suka taru suna mashi marhabin.

Paparoman yace Kirista da Musulmi a Lebanon suna zama tare shekara da shekaru kuma akwai iyalai da dama da suke da dangi daga dukan addinan biyu. Yace “idan haka tana iya yiwuwa a cikin iyali daya, menene zai hana a zauna lafiya da juna a tsakanin al’umma baki daya?”

Daya daga cikin shugabannin kasar Lebanon a wurin taron, Sheikh Rachid Qabbani, ya ba Paparoma Benedict wata wasika inda yace, yana daukar kaiwa kirista daya hari a a matsayin kaiwa dukan Musulmi hari.ya da sasantawa tsakanin Kirista da Musulmi.