Panda Bei Bei Ya Tafi China Domin Yada Zuri'a

Bei Bei

Bei Bei zai tafi yawon duniya, da fatar samo mata a kasar China.

Bayan kwashe watannin biyu ana shirye-shiryen yin ban-kwana da shi, matashin dabban nan jinsin Panda da ake kira Bei Bei, ya kama hanyarsa ta zuwa China.

Masana kimiyya na fatar matashin ya taimaka wajen samun karuwar hayayyafar nau'in wannan jinsi na Panda a can kasar ta China.

Bei Bei mai shekaru 4 da haihuwa, zai koma kasar shi ta gado, a cewar hukumomin gidan ajiyar namun daji na kasa a nan birnin Washington Gundumar Columbia.

Tafiyar Bei Bei Cirani

Sunansa na Bei Bei ya samo asali ne daga harshen Mandarin na China, wato abin da ke nufin, “kyauta daga Allah.”

Sun kuma tabbatar da cewar an saka shi a cikin wani katon keji, aka kuma saka mishi nau’ukan abinci uku da ya fi so wanda zai ta ci a tsawon tafiyar sa’o’i 16 da zai kwashe kafin su kai China.

“Yau wata rana ce ta juyayi a gare mu” a cewar shugaban gidan Zoo din Steve Monfort, muna kaunar Bei bei matuka da ma miliyoyin masu zuwa ziyara gidan, mun rene shi har ya kai wannan matsayin wanda muke sa ran ya zama jakada a cikin jinsin Pandoji.

Lokacin Da Aka Haifi Bei Bei Da Kaninsa

A wani shiri da muke da shi na kiwon namun daji, don gujewa bacewar na’ukansu, mun tabbatar da cewar jinsin Panda ba su cutarwa hasali ma rayuwarsu na cikin hatsari.

Akwai kididdigar da ke nuna cewar ana da sauran jinsin Panda 1,800 a duniya.

Bei Bei dai ba shi ne na farko a cikin danginsa da ya fara tafiya kasar waje ba, iyayen shi Mei Xiang da Tian Tian, sun isa kasar China a shekarar 2000, kana babban wansa Tai Shan da Bao Bao sun taba zuwa China lokacin suna matasa.

Baban Bei Bei

Yanzu haka iyayen Mei Xiang da Tian Tian masu shekaru 20 da haihuwa sune dattawa a jinsin Panda.

Gidan zoo din dai tare da hadin gwiwar masana kimiyya na kasar China na aiki kafada-da-kafada don ganin ba’a bar nau’in dabbobin ya bace a doron kasa ba.

Tun a shekarar 1972 aka fara wannan shirin lokacin da tsohon shugaban Amurka Richard Nixon ya ziyarci China.