Pakistan Ta Kaddamar Da Wata Manhajar Wayar Zamani

Muhammad Ashraf shugaban kwamitin bincike

Muhammad Ashraf shugaban kwamitin bincike

Pakistan ta kaddamar da wata manhajar wayar zamani da zata dinga sanar da mahukunta labarin ayyukan ta'addanci da masu tsatsauran ra'ayi da masu furta kalaman kiyayya saboda harzuka tada hankali

Pakistan ta kaddamar da wata manhajar wayar zamani da zata baiwa yan kasar damar bada labarin ayyukan ta’addanci da masu tsatsaurin ra’ayi da masu yada bayanai na kiyayya da zasu haddasa rarrabuwar kawuna ta kiyayya ba tare da an gano mai bada labarin bag a hukumomin kasar.

Wannan Mahajan da ake kira Chaukus wato lura, hukumar yaki da ayyukan ta’addanci ta NACTA ta kirkiro, itace hukumar kasar dake kula da shirya dabarun yaki da ta’addanci kuma ana samun manhajar a kan wayoyin zamani na Andriod da IOS.
Manhajar Chaukus da aka kirkiri a bara karkashin hukumar NACTA domin kyautata harkokin yanar gizo a kasar, zata kuma yaki ayyukan ta’addanci da kiyayya ta yanar gizo a cikin kasar.
Ministan harkokin cikin gida a Pakistan Ahsan Iqbal ya kaddamar da Chaukus a helkwatan hukumar NACTA a Islamabad a makon da ya gabata.