Pakistan Na Shirin Korar Jakadan India A Kasarta

A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Pakistan ta fidda, ta ce an sanar da gwamnatin India cewa Pakistan ba za ta tura sabon jakadan da aka nada zuwa India ba.

Kasar Pakistan, ta ce zata kori jakadan kasar India, dake can birnin Islamabad, ‘yan sa’o’i bayan da Pakistan din, ta rage yawan harkokin diflomasiyya, da cinikayyar da ta ke yi da Indiya, a sanadin kudurin India na cirewa yankin Kashmir, rigar matsayinsa na musamman, na yanki mai cin gashin-kansa.

Haka kuma, a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Pakistan, ta fidda, ta ce an kuma sanar da gwamnatin India, cewa, Pakistan ba za ta tura sabon jakadan da aka nada zuwa India ba.

Tun da farko, wata sanarwar Pakistan, ta ce, an kira wani babban taron gaggawa na kwamitin tsaro, na kasar, da ya hada da manyan shugabannin fararen hula, da hafsoshin sojoji, inda kuma, aka yanke shawarar rage matsayin, dangantaka tsakanin kasashen biyu, a matsayin matakin maida martini, akan matakan da gwamnatin Indiya ta dauka, ba bisa ka’ida ba.