Omoyele Sowore Na Fuskantar Tuhumar Cin Amanar Kasa

Omoyele Sowore

Shahararren dan jaridar Najeriyar nan kuma dan gwagwarmaya Omoyele Sowore, a yanzu yana fuskantar tuhumar cin amanar kasa. Bayan da ya kwashe tsawon watanni a gidan kaso.

Omoyele Sowore, wanda ya kirkiro kafar yada labaran yanar gizo ta "Sahara Reporters" ya bayyana a gaban babbar kotun tarayya dake birnin Abuja a jiya Laraba, kuma an ba shi ranar da zai koma kotu don sauraren karar sa a watan Afrilu.

A can baya dai hukumar tsaron Najeriya ta SSS mai binciken sirri da yaki da ta’addanci, ta kama shi a watan Agusta.

An kama Sowore ne bayan da ya shirya wani gangamin neman juyin juya hali mai taken "Revolution Now", bisa hujjar rashin adalci a babban zaben kasa da aka gudanar bara. An sake shi a ranar 5 ga watan Disamba, aka kuma sake kama shi washe gari, kana aka sake shi a ranar 24 ga watan na Disamba, bisa umarnin ministan shari’a na kasar.

Matar Sowore ta fadawa muryar Amurka cewa ana azabtar da shi ne saboda fadar gaskiya da ra’ayinsa.