Ofishin PDP Na Kasa Na Cigaba da Kasancewa A Rufe

PDP

Ofishin PDP dake Wadata Plaza a Abujan Najeriya ya cigaba da zama a rufe biyo bayan darewar jam'iyyar gida biyu inda kowane bangare ya kafa tasa hedkwatar a birnin na Abuja.

Bangarorin tuni suka kafa ofisoshinsu a Wuse II da Maitama daga inda kowannensu ke ikirarin shi ne halal.

A cikin wannan halin ne gwamnan jihar Ondo Mimiko ya garzaya zuwa wurin shugaba Buhari yana neman shugaban ya shiga tsakanin takaddamar da ta taso a jiharsa. Gwamnan ya nuna damuwa bisa umurnin da wata kotun tarayyar Najeriya ta bayar na tsayar da Ibrahim Jimoh na bangaren Modu Sheriff a matsayin dan takarar gwamnan Ondo a karkashin PDP a zaben ranar 26 na wata mai zuwa.

Tun farko bangaren Ahmed Makarfi ya tsayar da Eyitayo Jegede bangaren da shi gwamnan yake ciki to amma sai kotu ta dakatar dashi ta maye gurbinsa da Ibrahim Jimoh na bangaren Modu Sheriff lamarin da gwamnan yake ganin zai kawo yamutsi a jihar.

Tsohon mai ba tsohon shugaban kasa Jonathan shawara ta fuskar siyasa wato Ahmed Gulak yace kamata yayi bangarorin biyu na PDP su maida wuka cikin kube su kuma sauko daga dokunansu. Yace maganar kotu ba ita ba ce ta kamata a yi. Ya kira da a yi sulhu. Duk abun da za'a yi a samu nasara ya kamata bangarorin su yi.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Ofishin PDP Na Kasa Na Cigaba da Kasancewa A Rufe - 3' 28"