Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya Ya Shirya Taron Bunkasa Kananan Sana’o’i a Kano

Wasu cikin wadanda suka kasance a taron

Ofishin jakadancin Amurka dake Abuja ya shirya taron tattara ra’ayoyin jama’a kan yadda za’a habaka harkokin kananan kasuwanci tsakanin matasan arewacin Najeriya

Ofishin jakdancin Amurka a Najeriya ya shirya taron jin ra’ayi da tattaunawa a Kano, kan hanyoyin bunkasa kananan sana’o’i da kasuwanci a tsakanin matasan yankin arewacin Najeriya.

Masana harkokin kasuwanci da hada-hadar kudade, da manyan ma’akatan gwamnati da sukayi ritaya da kwararru a fannoni daban daban ne suka halarci taron baya ga dinbin matasa da masu sana’o’i daban daban, shugabannin gwagwarmayar raya tattalin arziki a tsakanin al’umma da dai sauransu.

Mr David Young, babban Jami’in diplomasiyya a ofishin Jakadancin Amurka dake Abuja, wanda ya jagorancin taron, ya bayyana farin ciki kan yadda ya ji bukatun masu kananan sana’o’i da kuma yadda za’a tallafa musu raya sana’o’in nasu.

Batutuwan da aka tabo a taron sun hada da maganar samar da lantarki da kyakkyawan yanayin gudanar da al’amura, nagartattun manufofi da tsare tsaren gwamnati, ilimantar da ‘yan kasa da ba su horo kan hanyoyin habaka kananan sana’ao’i da lamuran saka jari a tsakanin al’umma, da dai sauransu.

Baya ga wadannan matsaloli, Hajiya Aisha Kwaku, guda cikin wadanda sukayi jawabi a ya yin taron tace rashin fitar da jadawali na daga cikin kalubalen bunkasa sana’o’i a lardin arewacin Najeriya.

Bakin mahalarta taron ya daidaitu wajen hada karfi da karfe tsakanin al’uma da gwamnati da kuma kungiyoyin tallafi domin ceto arewacin Najeriya daga yanayin fatara ta yadda za’a murkushe miyagun ayyuka.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya Ya Shirya Taron Bunkasa Kananan Sana’o’i a Kano - 3' 17"