Dr. Junaidu Muhammad tsohon dan siyasa a jamhuriya ta farko na cikin wadanda suke zargin shi Farfasa Osinbajo da nuna kabilanci da bangaranci a nade naden da yayi.
Tsohon dan siyasan na mai cewa Shugaba Buhari, wanda yace bai san komi a harkokin tattalin arziki ba ya ba mataimakinsa dama ya kula da fannin. Ta dalilin haka ne shi Farfasa Osinbajo ya nada yawancin masana tattalin arziki daga inda ya fito, kusan kashi casa'in na mutanen daga bangarensa suka fito.
Amma ofishin Mataimakin shugaban yayi watsi da zargin. Alhaji Hafisu Ibrahim mataimaki na musamman ga Farfasa Osinbajo yace mutane masu cecekuce da basa son zaman lafiya suke zargin domin su kawowa mataimakin shugaban kasa batanci.
Dangane da cewa a wani kwamitin mutane tara, bakwai cikinsu Yarbawa ne, Hafisu Ibrahim yace ba nadasu aka yi ba ofishin da suke rike dashi ya basu kujerun.
Akan wai Farfasa Osinbajo yana take-taken neman shugaban kasa Alhaji Ibrahim ya musanta wannan ma.Yace a tarihin Najeriya babu wanda aka baiwa dama irin damar da aka bashi. Da yana da halin karbe shugabanci da tuni an gane.
Akan rabawa abokansa 'yan arewa sukari da wasu kayan masarufi lokacin azumi, Alhaji Ibrahim yace ya san mahimmancin azumi saboda haka idan ya raba masu kaya ba siyasa ba ce.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5