Odion Ighalo Yayi Bajinta A Gasar FA

Tsohon dan wasan Najeriya Odion Ighalo

Tsohon dan wasan Najeriya Odion Ighalo, ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin kungiyar sa ta Manchester United, ta sami gurbi a zagayen kungiyoyi takwas da za'a buga na gasar kwallon kafa ta cin kofin FA ta Ingila.

Ighalo ya nuna bajintarsa ta hanyar zura kwallaye biyu, wanda ya kai Manchester United ta samu nasara a kan Derby County da ci 3 da babu a wasan da suka yi a ranar Alhamis, a gasar cin kofin FA na Ingila zagaye na biyar.

Tun dai a watan Janairun bana ne Ighalo ya koma Manchester United, a matsayin aro, daga kungiyar Shanghai Shenhua ta kasar China, wanda tun bayan isar sa ya ke taka rawa soasi.

Tsohon dan wasan Super Eagles din, ya yi amfani da wata dama da ya samu na zura kwallo, jim kadan bayan fara wasan kafin tafiya hutun rabin lokaci, wanda hakan ya bai wa kungiyar ta United damar shiga zagaye na gaba.