Hukumar zabe a jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya ta ayyana gwamna Godwin Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben jihar.
WASHINGTON, D.C. —
Alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, Obaseki na jami’yyar PDP ya samu kuri’a 307,955 yayin da babban abokin hamayyarsa Osagie Ize-Iyamu na jam’iyyar APC ya samu kuri’a 223,619.
Rahotanni sun yi nuni da cewa PDP ta lashe 14 daga cikin kananan hukumomi 18 da jihar ke da su.
Obaseki mai shekara 63 ya lashe zaben ne a wa’adi na biyu.
A shekarar 2016 ya lashe zabe karkashin jam’iyyar APC.
A watan Yunin 2020 Obaseki ya koma jam’iyyar PDP daga jam’iyyar APC.
Bayanai sun yi nuni da cewa, gwamna Obaseki da abokin hamayyarsa Ize-Iyamu mai shekara 58 duk sun ci mazabunsu a wannan zabe.
Akalla 'yan takara 14 ne suka nemi kujerar gwamnan a jihar ta Edo mai kananan hukumomi 18.