Obama Ya Tsuma Dalibai A Jami'ar Howard.

Shugaban Amurka Barack Obama a bikin yaye dalibai a jami'ar Howard dake nan Washington DC.

Daliban su 2,300 ne suka sauke karatunsu a wannan shekara.

Asabar, shugaban Amurka Barack Obama, ya gabatar da jawabi mai tsumarwa ga dalibai da suke sauke karatu a jami'ar Howard wacce ta bakar fata ce, ya gayawa daliban cewa dangantaka tsakanin jinsuna a Amurka ta inganta sosai cikin shekaru 30 da suka wuce, duk da haka yace da sauran aiki.

"Ata ko wani fanni ka dubi Amurka yanzu, tafi lokcinda na sauke karatu," Mr. Obama ya gayawa daliban da suke sauke karatu a bana. Duk da haka shugaban, wanda shine bakar fata na farko da zai jagoranci Amurka, yace, har yanzu akwai wariyar launin fata, har yanzu akwai gibi idan aka duba yadda ake daukar mutane aiki,da albashinsu, da kuma fannin shari'a.

Haka nan Mr. Obama, ya gayawa msu sauke karatun anan birnin Washington cewa,idan suna bukatar ganin canji, "ba barci zasu yi ba," tilas su zage danste a dama su.

Shugaban na Amurka ya gayawa matasan cewa, basu da wata hujja na kin yin zabe. "ba zaku sadaukar da rayuwarku domin ku kada kuri'a ba," wasu sun rigaya sun yi muku wannan," Mr.Obama yayi kira ga masu sauke karatun, su 2,300 cewa, su tabbata sun kada kuri'a ba domin ba a zaben shugaban kasa ba kadai amma duka zabubbuka.

Mr. yace, a 2014, mutane biyu cikin biyar ne kadai suka fito domin kada kuri'a. Wanda ya nuna koma baya idan aka kwatanta da zaben da aka yi a shekara ta 2012. Ya tambayi daliban ba su lura cewa hakan ya taimaka wajen irin walilan majalisa da yake aiki d a su ba.