Shugaba Obama Yace Tilas Kenya Ta hada Kan Kasar Sannan ta Kaucewa Kabilanci Domin Ci Gaba.

Shugaba Obama a wani dandalin taro a Nairobi Kenya.

Shugaban Amurka Barack Obama yace kasar kenya tana bakin gacci, tana fuskantar hadurra masu yawa, ga kuma alamun fa'idoji masu dumbin yawa.

Yau lahadi Mr.Obama ya bayyana irin hange da yake yiwa kasar da take gabashin Afirka, lokacinda yake jawabi a Nairobi babban birnin kasar, a karshen ziyarar kwanaki biyu da ya kai kasar mahaifinsa,inda suke karrama shi a zaman dansu, kamin ya tashi zuwa Habasha ko Ethiopia.

Shugaban na Amurka ya yaba irin ci gaba da kenya ta samu tun bayan samun 'yancin kai daga turawan Ingila a shekarar 1963, ciki harda kawo karshen mulkin jam'iyya daya, da kuma shawo kan mummunar tarzoma bisa sabanin akida data barke a shekara ta 2007, kuma ta addabi kasar na watanni masu yawa. Mr.

Obama yace mutan kenya "sun zabi tarihi ko mataki mai kyau ba dawwama kan mummunar gaba da aka yi a baya ba."

Shugaba yayi magana kan 'yanci ko mutunta marta, yace Kenya ba zata je ko ina ba, muddin tana kallon mata manya da kanana a zaman 'yan bora.
Haka nan Mr.Obama yace siyasar da aka ginata kan kabilanci, siyasa ce da tabbas zata wargaza kasa.