Obama ya gana da danginsa a Kenya

Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barck Obama ya isa kasar kenya bisa tsauraran matakan tsaro a ziyarar kwanaki biyu da zai kai kasar.

A jiya juma’a da yamma ne jirgin shugaban Amurkan mai suna 'Airforce One' ya dira a Nairobi babban birnin Kenya. Inda shugaban kasar Uhuru Kenyatta ya tarbe shi, daga nan suka wuce kai tsaye Otal din da zai sauka suka ci abincin dare da danginsa.

Ciki har da kishiyar kakarsa Mama Sarah da kuma ‘yar uwarsa Auma Obama. An dai kawata titunan Nairobi da cewar ya kawo ziyara zuwa tushensa. Abun birgewa a ziyarar itace yadda Obama zai taya karbar bakin taron Duniya akan Sana’o’i da za a yi karon farko a Afrika inda Obaman zai yi jawabi a yau Asabar.

Wannan ce ziyarar Obama ta farko a matsayin shugaban Amurka in ka dauke wacce ya taba kai wa Kenyar a lokacin yana Sanata a Amurka a 2006. Kenya dai ita ce mahaifar Mahaifinsa Mista Obama da aka Haifa a can kuma ya rasu a kasar bayan yayi aikin gwamnati a karkashin shugaban kasar Kenya na farko.

Ana sa ran ziyarar tasa na iya kawo sauyi a harkokin kasuwancin kasar ta Kenya, sannan za su tattauna matsalar tsaro shi da shugaban kasar Uhuru Kenyatta.