A bana ma, kamar sauran shekaru, 'yan jarida, da fitattun tsakanin al'uma anan Amurka ne, suka halarci liyafar cin abincin-dare, da kungiyar 'yan jarida da suke aiki a fadar white House suka shirya, anan birnin Washington.
Taron ne dama ta karshe da shugaban Amurka Barack Obama yake da ita, na yin barkwanci ga abokansa da 'yan hamayya a banagaren 'yan jarida, da majalisar dokoki.
A kalamai da ake fassarwa a zaman na goyon-baya ga 'yar takarar shugabancin Amurka Hillary Clinton, ta jam'iyyar Democrat, Mr. Obama yace "badi a dai dai wannan lokaci, wani mutum ne daban zai tsaya a wannan wuri, kuma zaton kowa ne ko wacece."
Mutumin nan da aka sani bashi da "jumurin caccaka," Donald Trump, bai halarci taron na bana ba. Ya halarci na bara, amma da alamun bai ji dadin barkwanci ko zolayar da shugaban Amurka ya auna akansa ba.
Mataimakin shugaban Amurka Joe Biden, da sakataren harkokin wajen Amurka John kerry, shugabar asusun bada lamuni na duniya Christine Legarde, da senata Bernie Sanders, dan takarar shugabancin Amurka, shima a karkashin jam'iyyar Democrat din, suna daga cikin wadanda suka halarci taron cin abincin.
Haka nan yan wasan kwaikwayo a fannin silima da kuma talabijin suna daga cikin wadanda suka halarci taron na bana.
Daya daga cikin dalilan taron, shine bada damar karo ilmi ga dalibai, da kuma bada lambobin yabo ga 'Yan jarida da suka yi fice.
Tun a wajajen shekara ta 1914 ne aka fara wannan biki.