Gwamantin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Malam Nasir El Rufa’i ta sallami ma’aikatan kananan hukumomi a jihar, a wani yunkuri na cewa gwamnati na kokarin gyara ga tsarin da ke haifar da yadda wasu kananan hukumomi ba sa iya biyan ma'aikatansu albashi.
Ma’aikatan da aka sallama daga aikin sun fito ne daga kananan hukumomin jihar. Sai dai Gwamnati ta nuna cewa mafi yawancin wadanda aka sallama din ritaya aka musu ba kamar yadda kalilan daga ciki aka koresu daga aiki ba.
A cewa gwamnati, wannan garambawul din zai bawa kananan hukumomin jihar damar biyan albashi ba tangarda, kamar yadda Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu Alhaji Sani Ja'afaru ya bayyana.
Insa ya kara da cewa yawancin wadanda aka yiwa ritaya sama da mutane dubu 3 sun zarce lokacin ritayarsu da akalla shekaru goma ba tare da sun yi ritayar ba. Da kuma bada tabbacin sun yi haka ne don dawo da martabar Jihar game da biyan albashi, ta yadda kananan hukumomin za su iya biyan albashi ba tare da kai ruwa rana ba.
Sai dai kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi ta NULGE ta koka tare da garzayawa gaban kotu don kalubalantar wannan mataki da suka ce sam bai dace ba, kamar yadda Shugaban kungiyar reshen Jihar Kaduna Kwamared Ibrahim Kalid ya bayyana.
Wakilinmu Isa Lawal Ikara ya aiko mana wannan rahoton da ke kasa cikin murya
Your browser doesn’t support HTML5