Alhaji Abdullahi Ibrahim ya zanta da Muryar Amurka inda ya bayyana cewa hukumarsa tayi nasarar gano kudade Naira Milyan biyar, da irin wadannann bata gari suka sace daga hanun wani bawan Allah, bayan da mutumin yayi amfani da lambar neman taimakon "ko-ta-kwana" tuntubar jami'an hukumarsa.
Kiran da mutumin ya yi ya sa jami'an NSCDC suka bi barayin har suka kwato yawancin kudin, wato miliyan hudu da dubu dari takwas. Washegari kuma suka samu sauran kudin.
Dangane da laifukan da ake aikatawa a Maiduguri Alhaji Abdullahi ya ce " wani sabon salo ne da aka shigo dashi cikin Maiduguri wanda kuma daga wata jiha ake shigowa.
Haka nan akwai masu yashe man fetur suyar ta bayan fage d a tsada, ko kuma suyarwa 'yan ta'adda.Wata mota da suka kama tana da tanki na musamman da aka kirkiro.
Batun littafan Majalisar Dinkin Duniya da aka kame, inji Alhaji Abdullahi Ibrahim a tashar Borno Express aka yi kamun. Ya ce mutanen sun saba yin hakan. Da zara an kawo littafan sai su debesu su kaisu kudancin Najeriya su sake masu kamanni kana su mayar dasu jihar Borno su sayar da tsada.
Akan wannan lamarin mutane biyu sun fada hannu amma hukumar na gudanar da bincike ta gano ma'aikatan gwamnati dake hada baki cikin aika aikar.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5